TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profileg
TRT Afrika Hausa

@trtafrikaHA

Afirka tsantsarta

ID:1560178770832678912

linkhttps://www.trtafrika.com/ha calendar_today18-08-2022 08:16:48

5,3K Tweets

43,0K Followers

24 Following

TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

An yaɗa wani hoton abincin karin kumallo da ke nuna kunu kaɗan a wani mazubi da kuma ƙosai ƙwaya uku ana zargin hukumar 'da wulaƙanta alhazai' bayan da suka biya N8m kudin Hajji, amma NAHCON ta ce ƙarya ce ake yi mata don ɓata mata suna.
trtafrika.com/ha/africa/huku…

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Kenya za ta soma zaman sauraren ƙararrakin jama’a a ranar Talata kan zargin take hakkin ɗan'adam da kuma cin zarafi da sojojin Birtaniya suka yi a kasar.

trtafrika.com/ha/africa/keny…

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Wani yaro ɗan shekara 17 mai suna Ilyasu Aminu Alkassim Khalil, a birnin Kano na Njeriya, ya ƙirƙiro wata na'ura da nufin taimaka wa makafi yin tafiya ba tare da sun yi amfani da sanda ba. Khalifa Aminu, ya ce wa TRT Afrika Hausa cewa yana son sauƙaƙa wa makafi wahalhalun tafiya

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Ƙasar Austria ta samu adadi mafi yawa na rahotannin nuna ƙyamar addinin Musulunci a bara tun bayan da ta soma tattara bayanai kan lamarin a shekarar 2015, a cewar wani rahoto.
trtafrika.com/ha/world/yamar…

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin kasancewa ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a raga a gasar lig ta ƙasar Saudiyya.
Ɗan wasan ya ci ƙwallaye biyu a wasan da ƙungiyarsa ta Al Nassr ta doke Al Ittihad da ci 4-2 a ranar Litinin.

Ronaldo ya ci jimillar ƙwallaye 35 a kakar bana.

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin kasancewa ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a raga a gasar lig ta ƙasar Saudiyya. Ɗan wasan ya ci ƙwallaye biyu a wasan da ƙungiyarsa ta Al Nassr ta doke Al Ittihad da ci 4-2 a ranar Litinin. Ronaldo ya ci jimillar ƙwallaye 35 a kakar bana.
account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Tsohuwar tauraruwar Kannywood Fatima Usman wadda aka fi sani da Fati Slow ta rasu, kamar yadda Shugaban Hukumar Tace FinaFinai ta jihar Kano Abba El-Mustapha ya bayyana a shafinsa na Facebook ranar Talata.

Ƙasar Aljeriya ce ta buƙaci a yi taron gaggawar bayan Isra'ila ta yi kisan kiyashi a Rafah, ko da yake ita ba wakiliyar dindindin ba ce a kwamitin majalisar. trtafrika.com/ha/world/kai-t…

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Jami'an tsaron Isra'ila sun yi arangama da Yahudawa mabiya addinin gargajiya a wurin bauta na Tsaunin Meron, wanda hukumomi suka rufe a wannan shekarar, saboda fargabar hari daga ƙasar Lebanon.

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta shigar da gwamnonin jihohin kasar 36 ƙara a gaban Kotun Kolin Kasar kan batun bai wa kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu. Mun duba ainihin abin da ya jawo wannan tarnakin.

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Burna Boy ya lashe kyaututtuka aƙalla 60 a fagen sana'arsa ta waƙa da nishaɗi, yanayin da ya kai shi ga samun matsayi a cikin fitattun mawaƙan Afirka. trtafrika.com/ha/lifestyle/s…

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Babbar Kotun Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta hana Aminu Ado Bayero ayyana kansa a matsayin sarki, tare da bai wa ‘yan sanda umarnin fitar da shi daga gidan sarki da ke Nasarawa har zuwa lokacin da kotun za ta soma sauraren ƙarar da aka shigar a gabanta. Karin Bayani:

Erdogan ya soki firaministan Isra'ila yana mai cewa: 'Netanyahu da abokansa da suke kisan gilla tare na kokarin tsawaita lokacinsu ta hanyar yi wa mutane kisan kiyashi yayin da suka kasa yin nasara a kan gwagwarmayar Falasdinawa.

trtafrika.com/ha/turkey/hare…

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada buƙatar ƙara ƙaimi wajen jan hankalin ƙasashen duniya da su amince da Falasɗinu a matsayin 'yantacciyar ƙasa. trtafrika.com/ha/turkey/jink…

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Isra'ilawa sun riƙa gudun tsira da rayukansu yayin da hukumomin Tel Aviv suka sanya jiniya don jan hankalinsu kan rokokin da ƙungiyar Hamas ta harba birnin a matsayin martani kan hare-haren da Isra'ila take kai wa Gaza.

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da aikin gina titin gaɓar teku mai tsawon kilomita 700 daga Lagos-Calabar da ke kudancin ƙasar.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da aikin ranar Lahadi a birnin Lagos, shugaban na Nijeriya ya ce yana sa rai za a kammala aikin a cikin shekaru

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da aikin gina titin gaɓar teku mai tsawon kilomita 700 daga Lagos-Calabar da ke kudancin ƙasar. Da yake jawabi yayin ƙaddamar da aikin ranar Lahadi a birnin Lagos, shugaban na Nijeriya ya ce yana sa rai za a kammala aikin a cikin shekaru
account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray da ke Turkiyya ta lashe gasar Super Lig karo na 24 bayan ta doke takwararta ta Tumosan Konyaspor da ci 3 -1 a fafatawar da suka yi ranar Lahadi.
trtafrika.com/ha/sports/gala…

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray da ke Turkiyya ta lashe gasar Super Lig karo na 24 bayan ta doke takwararta ta Tumosan Konyaspor da ci 3 -1 a fafatawar da suka yi ranar Lahadi. trtafrika.com/ha/sports/gala…
account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Gomman mutane sun mutu yayin da dama suka jikkata lokacin da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai hari kan tantunan 'yan gudun hijira da ke kusa da hedkwatar hukumar kula da Falasɗinawa 'yan gudun hijira (UNRWA) a Rafah da ke Gaza

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya ce wasu maƙiyan jihar ne suke so su yi amfani da rikicin sarauta da ke faruwa tsakanin Sarki Muhammadu Sanusi II da tsohon Sarki Aminu Ado Bayero domin hargitsa Kano baki ɗayanta. trtafrika.com/ha/africa/mun-…

account_circle